Za mu riƙa biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Edo—Obaseki

Daga Sodiqat Aisha Umar
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma’aikata a jihar.
Ya sanar da haka ne a wurin kaddamar da sabon ofishin kwadago a jihar Edo.
Gwamnan ya ce sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago ta ƙasa ke ta fafutukar ganin gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa.