October 18, 2025

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Bayan Tashin Hankali Da Aka Samu a Bauchi

FB_IMG_1734863288490.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da cafke mutum 15 da ake zargi da hannu a wani rikici da ya faru a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Ahmed Wakil, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.

A cewar Wakil, ana zargin wadanda ake tuhumar sun kai hari kan wasu fararen hula tare da lalata ofishin Ƙungiyar Sa-Kai (Civilian JTF) da ke kusa da Makarantar Firamare ta Kandahar.

“Masu tayar da zaune tsaye sun banka wa ofishin Civilian JTF wuta tare da wani ɓangare na Makarantar Firamare ta Gwamnati,” in ji Wakil.

Ya kara da cewa, “A lokacin rikicin, mambobin Civilian JTF sun fuskanci masu harin, wanda ya jawo raunin wani daga cikin su, mai suna Saidu Musa, ɗan shekara 22, wanda aka harba a ƙirji da bindigar hannu ta gargajiya.

“Domin magance rikicin, an tura tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin nan take, inda suka samu nasarar dakile rikicin tare da dauke Saidu Musa zuwa Asibitin Kwararru don kula da lafiyarsa.”

Binciken farko ya nuna cewa, “A ranar 18 ga Disamba, 2024, Civilian JTF sun fuskanci wasu matasa masu tashin hankali a unguwar Kandahar. Bayan haka, a ranar 19 ga Disamba, 2024, matasan suka sake haduwa suka kai hari mai tsanani kan ofishin Civilian JTF da makarantar firamare, inda suka lalata kayayyaki tare da razana fararen hula,” in ji Wakil.

Jami’in hulɗa da jama’a ya jaddada cewa saurin daukar matakin gaggawa da jami’an ‘yan sanda suka yi ya kawo zaman lafiya a yankin. Ya tabbatar da cewa an kama mutum 15 da ake zargi da hannu a rikicin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, Auwal Mohammed, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin abin da ba a yarda da shi ba. Ya yi kira ga al’ummar jihar Bauchi da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da mika ƙorafinsu ga hukumomin da abin ya shafa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda ya umarci Sashen Binciken Laifuka na Jihar (CID) da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

1 thought on “‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Bayan Tashin Hankali Da Aka Samu a Bauchi

Comments are closed.