Yaƙi tsakanin Hamaz da Isra’ila na ƙara ta’azzara al’amura a Gaza

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyaho ya gargaɗi ƙasashen ƙetare da su guji kawo tallafin gaggawa ga ƙasar Falasɗinu mazauna zirin Gaza, bayan daukan kwanaki biyar suna musayar wuta a tsakaninsu.
Amma tuni sakataren Majilisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi fatali da wannan batu na Mista Benjamin, inda ya sanar da cewa a halin yanzu Falasɗinawa suna buƙatar agajin gaggawa wanda ya haɗa da abinci, ruwa, magani, da sauran abubuwan amfani na yau da kullum don rage raɗadi.
Ana sa rai ƙasashen ƙetare za su fara kai musu tallafi, don wata maƙala wadda wani babban malami, Omar Suleiman, ya rubuta a shafin shi na yanar gizo ya tabbatar da cewa an yanke wuta da ruwa a cikin zirin Gaza da yake Falasɗinu.
Sannan suna da mutane da dama wadda suna ƙwance a asibiti suna buƙatar agaji na gaggawa da kulawa ta musamman, inda ya ƙara da cewa kimanin mutum dubu ne suka rasa rayukansu, mafi yawanci a cikin waɗanda suka rasa rayukan nasu yara ne ƙanana.
Bugu da ƙari duk wata ƙafa da za a taimaka wa Falasɗinu ta ko’ina an toshe.