October 18, 2025

Tinubu ya ba wa ɗan Ganduje muƙami

IMG_5050.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Umar Abdullahi Umar a matsayin sabon Babban Darakta na Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara.

Umar dai ɗa ne ga tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa a yanzu.

An sanar da naɗin nasa ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ɗauke da sa hannun mai baiwa Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, a ranar Alhamis.

Nadin ya biyo bayan dakatar da Ahmad Salihijo Ahmad, tare da wasu manyan daraktocin hukumar uku daga aiki.

Wannan nadin dai ya gamu da suka daga ƴan Najeriyar saboda ana ganin akwai nuna rashin azanci a ciki.