October 18, 2025

TCN ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta gyara matsalar wutar lantarki a Arewa ba

IMG-20241025-WA0006.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar Rarraba Wutar Lantarki a Najeriya (TCN) ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba su samu damar gyara wutar lantarki da rashinta ya addabi Arewacin Najeriya ba.

A cewar hukumar, sun sami takardar gargaɗi ne daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, inda aka nuna cewa haɗari ne shiga yankin da aka lalata manyan turakun lantarki guda uku ɗin saboda matsalar tsaro a wurin.

Babbar jami’ar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), Nafisatu Asabe Ali, ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a.

Ta ƙara da cewa, duk da cewa kamfanin ya tanadi kayan aikin gyaran layin lantarki, ba zai iya shiga yankin domin gyara ba har sai an samu zaman lafiya a wurin.

Zuwa yanzu dai wannan matsala ta shafe mako guda ke nan, inda lalacewar babban layin lantarki na Shiroro zuwa Manzo ya haifar da katsewar wutar lantarki ga yawancin jihohin Arewa.

Nafisatu Asabe Ali dai ta ce har yanzu ba za a iya bayyana takamaiman lokacin da za a kammala gyaran ba saboda matsalar tsaron.

TCN ta bayyana cewa wannan matsala ta jefa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da wani ɓangare na Arewa ta Tsakiya cikin matsi na rayuwa.