October 18, 2025

NDLEA ta kama wata mata da ke wa ƴan bindiga safarar alburusai

image_editor_output_image1042124351-1704638065364.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (watau NDLEA) ta ce ta kama wata mata Bilkisu Suleman mai shekaru 28 da ke yi wa ‘yan bindiga safarar harsashi.

Fuskar Bilkisu ke nan

Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na hedikwatar NDLEA a Abuja, Femi Babafemi, a wata sanarwa a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu, ya ce sunan Bilkisu ya zo cikin jerin sunayen wasu mutane 12 da jami’an hukumar ta NDLEA suka kama a yayin gudanar a wannan sabuwar shekara.

Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama Bilkisu ne a ranar Laraba 3 ga watan Janairu a kan hanyar Zariya zuwa Kano dauke da alburusai 249 mm 7.62 da aka boye a cikin wata bakar ledar nailan.

NDLEA ta yi zargin cewa tana kan hanyarta ne ta kai harsashin ga wani dan bindiga da aka gano a kauyen Kakumi, jihar Katsina, a lokacin da aka kama ta.

Sannan daga bisani aka mayar da ita wajen ‘yan sandan jihar Kaduna domin ci gaba da bincike.