October 18, 2025

Matatar mai ta Dangote ta fara sayar da fetur kai-tsaye ga ƴankasuwa

FB_IMG_1729224212516.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Matatar mai ta Dangote ya fara sayar da man fetur kai tsaye ga masu kasuwanci ba tare da amfani da Hukumar Man Fetur ta Kasa (NNPC) ba.

Rahotanni sun nuna cewa yayin da ƴan kasuwar da dama ke neman sayen fetur kai tsaye daga gidan, wasu suna shigo da man daga waje.

Sai dai ana sa ran cewa adadin fetur da aka shigo da shi zai iso Najeriya cikin makonni biyu masu zuwa.

Hukumar Jiragen Ruwa ta Najeriya ta tabbatar cewa tsakanin ranar 18 da 20 ga Oktoba, wasu jiragen ruwa da suka ɗauki man fetur sun sauka a tashoshin ruwa, sun kuma kawo kimanin miloni 123.4 na fetur don inganta samar da mai a fadin ƙasar.

Yayinda sayarwa kai tsaye ta fara, manyan masu kasuwanci suna fara samun fetur daga gidan mai na Lekki. Wani jami’in gidan mai ya bayyana cewa ana gudanar da kasuwancin ne bisa ka’idar wanda ya sayi, wanda ya sayar, duk da cewa bayani kan farashi ba a bayyana shi ba.

Duk da gwamnatin tarayya yanzu tana bayar da danyen mai ga matatar, akwai alamu na inganta ayyukan. A halin yanzu, kusan kashi 53% na danyen mai da take samarwa ana amfani da shi ne wajen samar da man fetur, tare da yiwuwar sauyawa bisa ga bukatar sauran kayayyakin.