Allah Ya yi rasuwa wa tsohon firaministan Nijar Hama Amadou
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon Firaministan Jamhuriyar Nijar, Hama Amadou, ya rasu a daren Laraba bayan fama da jinya, kamar yadda wasu daga cikin makusantansa suka tabbatar.
Rahotanni sun bayyana cewa Hama Amadou, wanda ya taba shugabancin majalisar dokokin Nijar, ya rasu ne a kan hanyarsa ta zuwa babban asibitin birnin Yamai.
An haifi marigayi Hama Amadou a ranar 3 ga watan Maris, shekarar 1950, a garin Youri da ke cikin jihar Tillabery, yankin yammacin Nijar, yana da shekaru 74 a lokacin rasuwarsa.