Matakin BRICS na rubuta sunan Najeriya da harshen Hausa a kan takardar kuɗinta ya janyo zazzafar muhawara

Daga Sabiu Abdullahi
An samu zazzafan cece-kuce tun bayan matakin da aka ɗauka na rubuta sunan Najeriya da harshen Hausa, watau “Jamhuriyar Tarayyar Najeriya”, a kan takardar kudin BRICS da ake shirin fitarwa.
Wannan mataki ya haifar da martani daga wasu sassan Najeriya, musamman daga kudancin Najeriya, inda galibin masu sukar suke.
Daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu game da lamarin, wasu na ganin ganin kuskure aka yi, yayin da wasu kuma ke ganin an yi daidai.
Daga cikin masu ganin an yi daidai akwai tsohon mai taimaka wa Shugaba Buhari, Bashir Ahmad. Ya yaba da wannan mataki.
A bangare guda kuma, David Hundeyin, wani sanannen mai amfani da kafar X, watau Twitter, ya yi suka ga matakin inda ya ce:
“Rubuta ‘Nigeria’ da Hausa a kan kudin BRICS yana nuna abubuwa uku. Na farko, hakan ya tabbatar da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta matsa lamba akan neman shiga BRICS. Buhari bai taba yin wani abu na alheri ba tare da jawo rikici ba. Ya kaucewa amfani da harshen hukuma na kasar Najeriya, sai ya sanya harshen kabilarsa a kudin, wanda ya dace da yadda ake tsammanin Muhammadu Buhari zai yi. Wannan abu ne na kunyatawa ga Najeriya.”
“Na biyu, gwamnatin Tinubu ba ta da hannu a cikin wannan lamarin, kuma ana iya cewa tana karkashin umarnin wata babbar hukumar waje domin lalata shirin Najeriya na shiga BRICS.
“Na uku, Najeriya bata halarci taron BRICS da ake yi ba a wannan shekara. Babu shugaban kasa, mataimaki ko ministan harkokin wajen Najeriya a wurin taron. Wannan babban al’amari ne da ya nuna akwai abin da ke faruwa a bayan fage.”
Cece-kucen ya fi fitowa ne daga kudu, inda ake ganin harshen Hausa ya fi yawa a arewacin kasar, don haka wasu sun yi suka da cewa bai dace a kaucewa amfani da sauran harsunan Najeriya a irin wannan babban shiri ba. Haka kuma, wasu na ganin cewa wannan lamari na iya yin tasiri akan shirin Najeriya na shiga cikin kungiyar BRICS.
Akwai yiwuwar masu sukar abin sua ci gaba da bibiyar wannan lamari domin ganin ko Najeriya za ta dauki wani mataki kan wannan batu.
BRICS dai wata kungiya ce ta kasashen duniya biyar wato Brazil, Rasha, Indiya, China, da Afirka ta Kudu, waɗanda suka haɗu don ƙarfafa haɗin kai da ci gaban tattalin arziki a tsakanin su.
Kungiyar tana nufin inganta cinikayya da saka hannun jari a tsakanin kasashen mambobinta, tare da rage dogaro da kasashen Yamma.
A ‘yan kwanakin nan, kungiyar BRICS ta fitar da shawarar fara amfani da sabuwar takardar kudin bai ɗaya, wanda ya haifar da cece-kuce musamman a Najeriya, bayan sun rubuta sunan kasar a matsayin “Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.”
I hsve to thank youu ffor thee eftorts youu have put in writing this blog.
I really hop to see the same high-grade contednt bby
you inn the futue as well. In truth, your creatrive writing
abilities has eencouraged mee to get my own, pesonal website now 😉
Its nott mmy first time tto pay a isit this webb site, i am visiting thos site daiklly and geet pleasant information from here daily.