January 15, 2025

Tinubu ya umurci ministocinsa da su rage adadin motoci da jami’an tsaron da ke biye da su a ayarinsu

0
images-14-28.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin cewa ministoci, ƙananan ministocin, da shugabannin hukumomin gwamnati su takaita yawan motocin ayarinsu zuwa uku kacal.

Wannan matakin, wanda mai ba wa shugaban shawara na musamman, Bayo Onanuga, ya sanar a jiya Alhamis, an ɗauke shi ne don rage kudin gudanar da ayyukan gwamnati.

A cewar Onanuga, “Shugaba Bola Tinubu ya takaita ministoci, ƙananan ministocin, da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya daga amfani da motoci da yawa, sai dai uku kacal a ayarinsu na aiki. Babu wata mota da za a ba su don karin amfaninsu.”

Umarnin ya kuma tanadi cewa kowane jami’i zai samu ma’aikatan tsaro biyar ne kacal, wanda ya kunshi ‘yan sanda hudu da kuma jami’in Hukumar Tsaro ta DSS guda ɗaya.

Wannan mataki na rage kudin gwamnati ya biyo bayan wasu tsare-tsaren rage kudade da aka dauka a baya, ciki har da rage yawan ma’aikatan da ke tafe da Shugaba Tinubu a tafiye-tafiye na kasashen waje daga mutum 50 zuwa 20, yayin da a cikin gida aka rage zuwa mutum 25.

Hakazalika, an rage ayarin Mataimakin Shugaban Kasa zuwa mutum biyar a tafiya ta kasashen waje da kuma mutum 15 a cikin gida.

Shugaba Tinubu ya umurci mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa da ya tattauna da hukumomin soji, faramilitiri da sauran jami’an tsaro domin tantance yadda za a rage motocin da ma’aikatan tsaro da za su rika tafiya da manyan jami’ai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *