Kotu Ta Tsare Mutane 4 Masu Alaƙa da Bello Turji Kan Zargin Ta’addanci

Daga Sabiu Abdullahi
A ranar Litinin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin cigaba da tsare wasu mutane hudu da ake zargi da alaka da Bello Turji, shahararren shugaban ƴan fashin daji, a gidan yarin Kuje.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan da waɗanda ake zargin suka musanta tuhume-tuhume 11 da ake musu waɗanda suka shafi aikata ta’addanci.
Mai shari’a Nwite ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2025 domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya bayyana cewa mutanen da ake zargin sun haɗa da Musa Muhammad Kamarawa; Abubakar Hashimu, wanda aka fi sani da Sakta; Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma. Dukkaninsu sun musanta tuhume-tuhumen 11 da aka karanta musu a kotun.
A baya, NAN ta ruwaito cewa an jera sunayen mutane takwas cikin tuhume-tuhumen, amma uku daga cikinsu, har da Bello Turji, sun tsere. Sai dai lokacin da aka kira shari’ar, hudu ne kawai aka gabatar a gaban kotun.
Avcılar su kaçak tespiti Doğal Kaynakları Koruyan Çözüm: Kaçak tespiti sonrası su israfının önüne geçtik. Harika bir hizmet. https://harbornaz.org/author/kacak/
I loke the helpfl information you provide inn your articles.
I’ll bookmmark youir wwblog annd checfk agan here regularly.
I am quite certain I’ll lewarn manyy neew stuff rght here!
Good luck ffor tthe next!