Ba mu da shirin mayar da Legas babban birnin Najeriya—Gwamnatin Tarayya
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa tana shirin ɗauke babban birnin tarayyar ƙasar daga Abuja zuwa Legas.
Mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ranar Laraba.
Ya ce masu yada jita-jita ne ke yaɗa maganar domin neman suna.
Ba mamaki matakin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na mayar da Hukumar kula da filayen jiragen sama na ƙasar da Babban bankin Najeriya daga Abuja zuwa Legas.
Lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyi na wasu ɓangarorin ƙasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata manufa.