October 18, 2025

Kotu ta ba da umurnin kama Dr. Idris Dutsen Tanshi

FB_IMG_1705634794764.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa daga Arewacin Najeriya na nuna cewa kotun Shari’ar Musulunci a jihar Bauchi ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi a kowanne lokaci za a iya kamo shi.

Kotun dai ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris ɗin takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Rahotanni sun ambato Barista Ahmad Musa Umar, wanda shi ne lauyan Dr Idris, yama cewa “kotu za ta iya bai wa ‘yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci.

“Kotun ta ce ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami’an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana.”

Tun a baya dai Dr. Idris yake da sa-in-sa da gwamnatin Jihar Bauchi ta Bala Mohammed Abdulkadir.

Lauyan Dr. Idris ya ce malamin ya yi zaman gidan yari na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli.