October 18, 2025

Kotu ta ƙara damƙa wa Natasha kujerar sanata a Kogi

Copy-of-Copy-of-sr-file-81.jpg

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jihar da ta bayyana Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaben Sanatan Kogi ta Tsakiya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ranar 6 ga Satumba, 2023 ne dai kwamitin mutane uku na kotun sauraron ƙararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a K.A. Orjiako a hukuncin da ya yanke ya ce Uduaghan ta samu kuri’u 54,064 inda ta doke abokin hamayyarta Sadiku-Ohere na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 51,291.

Kotu ta ci tarar Ohere N500,000 da za a biya Akpoti-Uduaghan.

‘Yar takarar ta jam’iyyar PDP ta shigar da ƙararta a kotun sauraron ƙararrakin zabe ta kasa da ta jiha, inda ta zauna a Kogi tana kalubalantar ayyana Ohere a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ta kuma nemi a ba da sanarwar cewa ita ce ta lashe zaɓen kuma ya kamata a ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara a zaben bayan ta samu mafi rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen.