October 18, 2025

Isra’ila Ta Kai Wa Iran Farmaƙi, Ta Kashe Manyan Jami’an Soji Da Masana Kimiyya

images (49)

Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a cikin dare a birnin Tehran, babban birnin Iran, inda ta kashe wasu manyan kwamandojin soji da masana kimiyya, ciki har da shugaban hafsoshin tsaron Iran, Mohammad Bagheri, da kuma Ali Shamkhani, babban mai ba jagoran addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei, shawara.

An fara jin karar fashewa a misalin karfe 4 na dare a birnin Tehran, lamarin da ya haifar da firgici ga mazauna garin. Isra’ila ta bayyana wannan farmakin a matsayin wani ɓangare na abin da ta kira Operation Zaki, wanda aka aiwatar domin tarwatsa cibiyoyin shirin nukiliyar Iran.

Ministan tsaron Isra’ila ya tabbatar da farmakin, inda ya ce sun kai hari ne don kare kasarsu daga barazanar Iran da kuma dakile yiwuwar ramuwar gayya daga ƙasar.

Hotunan bidiyo sun nuna hayaki yana turmuɗe daga sassan birnin Tehran, yayin da hukumomi ke kokarin shawo kan halin da ake ciki.

Baya ga jami’an tsaro, rahotanni sun ce harin ya rutsa da wasu yara kanana da ke kusa da wuraren da aka kai hare-haren.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce: “Mun kai hare-haren ne kan muhimman cibiyoyin nukiliya da sauran wuraren binciken kimiyya da Iran ke amfani da su don barazana ga makomar duniya.”

A gefe guda, gwamnatin Amurka ta nesanta kanta da harin, tana mai cewa babu hannunta a wannan mataki da Isra’ila ta dauka.

Farmakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa Isra’ila na shirin daukar mataki kan shirin nukiliyar Iran wanda ta dade tana zargin cewa ana amfani da shi ne domin ƙera makaman nukiliya.

Iran dai ba ta fitar da cikakken bayani ba game da adadin wadanda suka mutu, amma harin ya janyo fargaba da yuwuwar ƙarin rikice-rikice a yankin Gabas ta Tsakiya.

Za a ci gaba da sa ido kan martanin Iran da kuma tasirin wannan farmakin a siyasar duniya da kuma batun zaman lafiya a yankin.