IAEA Ta Janye Jami’anta Daga Iran Sakamakon Tsanantar Rikici

Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar Kula da Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta bayyana cewa ta janye jami’anta daga cibiyoyin nukiliyar Iran, sakamakon tsanantar rikici da ake fuskanta a ƙasar.
Rahotanni sun ce jami’an IAEA ba su sake samun damar shiga cibiyoyin domin sanya ido tun bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan da ya gabata.
Shugaban hukumar, Rafael Grossi, ya bayyana cewa, “sanya idanu kan cibiyoyin nukiliyar Iran shi ne babban muradin hukumar a ƙasar.”
Majalisar dokokin Iran ta kada ƙuri’ar dakatar da hulɗa da IAEA, sai dai ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa za a ci gaba da wasu ayyukan haɗin gwiwa da hukumar.
Sai dai hukumar IAEA ta ce har yanzu Iran ba ta sanar da ita a hukumance ba game da matakin dakatar da hulɗar.