October 18, 2025

Haaland Na Da Muhimmanci a Garemu—Guardiola

image_editor_output_image1951318201-1736021675003.jpg

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya jaddada muhimmancin dan wasan gaba, Erling Haaland, ga tawagar.

Yayin da yake jawabi gabanin wasan gasar Premier League da za su buga da Everton a ranar Boxing Day, Guardiola ya bayyana cewa Manchester City na bukatar amfani da damar da ke tare da dan wasan na Norway yadda ya kamata.

Haaland, wanda ya lashe Golden Boot a matsayin babban mai zura kwallaye a Premier League a bara, bai samu cin kwallo a wasanni uku na baya-bayan nan da ya buga wa tawagar Guardiola ba. Duk da haka, ya fara wannan kakar da karfi, inda ya ci kwallaye 14 cikin wasanni 13 a dukkan gasa.

Manchester United kuwa na duba yiwuwar daukar Victor Osimhen, yayin da alamu ke nuna cewa Marcus Rashford zai bar Old Trafford a watan Janairu mai zuwa.

Rashford ya rasa amincewar kocin Manchester United, Ruben Amorim, a makonnin da suka gabata. Dan wasan mai shekaru 27 bai samu shiga cikin jerin ‘yan wasan da suka taka leda a wasanni uku na baya-bayan nan ba.

Rashford ya riga ya nuna aniyarsa ta fara sabon babi a rayuwar kwallonsa.

Tsohon dan wasan tsakiyar Chelsea, Oscar, kuwa ya kammala komawarsa kulob din São Paulo bayan ya bar kulob din kasar Sin, Shanghai SIPG.

Fitaccen masani kan harkokin ƙwalln ƙafa, Fabrizio Romano, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.

1 thought on “Haaland Na Da Muhimmanci a Garemu—Guardiola

  1. I don’t think the title of your article matches the content lol. Just kidding, mainly because I had some doubts after reading the article.

Comments are closed.