Gwamna Soludo: “Inyamurai Ne Ke Da Alhakin Kashi 99 Na Ayyukan Ta’addanci a Kudu-maso-Gabas, Ba Fulani Ba”

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya bayyana cewa mafi yawancin laifukan ta’addanci da suka addabi yankin Kudu-maso-Gabas ‘yan kabilar Ibo ne ke aikata su, ba Fulani ba kamar yadda ake yadawa.
Soludo ya bayyana haka ne a yayin wani taro da aka gudanar da ‘yan asalin Anambra a birnin Maryland, Amurka.
Ya ce, kashi 99.99 cikin 100 na mutanen da hukumomi suka kama bisa laifukan garkuwa da mutane da kisan kai da sauran miyagun ayyuka a lokacin mulkinsa na tsawon shekaru uku da watanni uku, dukkansu ‘yan Ibo ne.
A cewarsa: “Wadanda ake kira masu ’yantarwa da ke boye a cikin dazuka ’yan gida ne masu aikata miyagun laifuka suna cin gajiyar kudin jini. Suna fitowa da ikirarin cewa su ne ke kare ku daga makiyaya Fulani.”
Ya ci gaba da cewa: “Suna zaune a daji na tsawon watanni, amma babu wanda ya taba tambaya yadda wadannan masu kiran kansu ’yan ’yantarwa ke rayuwa a daji. Dole ne su ci abinci, wa ke biya musu bukatun su, ashe ba su da bukatu?”
Soludo ya bayyana cewa akwai bukatar a fuskanci gaskiya game da halin da ake ciki a yankin, yana mai cewa: “Mu daina yaudara. Ibo ne ke yin garkuwa da mutane da kisan ’yan uwansu Ibo, ba Fulani ba.”
Jawabin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Kudu-maso-Gabas ke fuskantar matsaloli na tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, kisan gilla, da ayyukan ‘yan bindiga da ake alakanta da masu fafutukar kafa kasar Biafra.