Ba Za Mu Tattauna Da Amurka Ba Sai Isra’ila Ta Dakatar Da Kai Mana Hare-Hare—Iran

Daga Sabiu Abdullahi
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga kowace irin tattaunawa da Amurka ba har sai Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa a yanzu.
Wannan na ƙunshe ne cikin rahoton da kamfanin dillancin labarai na gwamnati, IRNA, ya fitar.
“Akwai saƙonni da dama daga Amurka suna neman mu shiga tattaunawa, amma mun bayyana a fili cewa babu wani gurbi na tattaunawa har sai wannan hare-haren ya tsaya,” in ji Araghchi yayin wata hira da kafar labarai.
Ya ƙara da cewa: “Ba mu da wani shiri na tattaunawa da Amurka kasancewar tana da hannu a wannan laifi.”
An bayyana cewa Araghchi na shirin ganawa da wasu ministocin harkokin wajen Turai a Geneva yau.
Wannan zama shi ne na farko da Iran za ta yi da wakilan ƙasashen yamma kai tsaye tun bayan da Isra’ila ta fara sabon rikici a makon da ya gabata.
Hare-haren da Isra’ila ke kai wa sun haifar da tashin hankali a yankin, kuma hakan ya sa dangantaka tsakanin Iran da kasashen yamma ta sake dagulewa.