October 18, 2025

Ba za a taɓa mutunta Afirka a idon duniya ba idan ba mu cire mutanenmu daga ƙangin talauci ba—Akinwumi Adesina

images-2023-11-29T082920.344.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Dr Akinwumi Adesina, Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB) ya ce Afirka ba za ta sami mutuntawa a duniya ba har sai mun kawo ƙarshen talauci zuwa wani ma’auni.

Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Talata, a Legas, a wajen bikin cika shekaru 40 na jaridar Guardian.

Da yake magana a laccar, Adesina ya ce tsawon lokaci, Afirka ta bar talauci ya ci gaba da kasancewa a cikin tsaka-tsakin wadata.

A cewarsa, talauci ba shi da kyau, musamman ma lokacin da albarkatun kasa suke.

Ya ce bai kamata Afirka ta zama gidan tarihi na talauci ba, yana mai cewa idan ana so a sauya wannan yanayin, dole ne a samar da bangaren da za a bi wajen tunkarar lamurran al’umma.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa a halin da nahiyoyin ke ciki a halin yanzu, Adesina ya ce ba dole ba ne talauci ya zama abin kwatance irin na Afirka ba, duk da kasancewar rabin zinare a duniya da kashi daya bisa uku na ma’adanai a duniya a nan suke.

“Dole ne gwamnatocinmu su gane cewa alhakinsu ne su fitar da dukkan al’ummarsu daga kangin talauci cikin gaggawa.

“Yana iya yiwuwa. Mun ga misalai ƙarara na irin wannan ci gaba a wasu yankuna na duniya, musamman a Asiya cikin shekaru talatin da suka gabata.

“Babu dalilin da zai sa ba za a iya kawar da matsanancin talauci a Najeriya da kuma fadin Afirka ba. Dole ne mu zama nahiya da ke samun wadatuwa tare da rarraba wadatar nan ga jama’a.”

Ta hanyar yin amfani da Koriya ta Kudu a matsayin misali, Adesina ya ce kasar ta tashi daga GDP na kowane mutum wanda ya kai dala 350 a shekarun 1960 lokacin da ta samu ‘yancin kai, zuwa kusan dala 33,000 a shekarar 2023.

“Dole ne mu tambayi kanmu, shin yaushe ne za mu yi canjin da Koriya ta Kudu ta yi daga kasancewa ƙasa wacce ta kasance mai matsaƙaicin matsayi na ci gaba zuwa ƙasa mai arziki, mai arzikin masana’antu da take a yau?

Da yake magana kan albarkatun, Adesina ya ce akwai wani abu da ba daidai ba ne a tsarin sarrafa albarkatun ƙasa.

Ya yi nuni da cewa, idan aka ci gaba da samun tabarbarewar albarkatun ƙasa, Afrika za ta ci gaba da kasancewa a maƙale cikin talauci.