October 18, 2025

An kashe wani mutumin Bauchi a lokacin da aka zo yi masa gwajin maganin bindiga

images-2023-11-08T121014.513.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

An harbe wani mutum mai shekaru 43 yayin da wani matsubbaci da wasu mutane uku ke gwada masa maganin bindiga a jihar Bauchi.

Marigayin mai suna Muhammadu Ali, mazaunin kauyen Damaiwa a Bursali a karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi, an ce ya je dajin Damaiwa ne tare da mutane hudu don gwada ko wata laya za ta kare shi daga harbin bindiga.

Sai dai kuma da aka harba bindigar a cikin gida domin a tabbatar da ingancin wannan laya, abin ya faskara, inda aka kashe shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya ba wa manema labarai a ranar Talata.

Ya ce a lokacin da ‘yan sanda suka samu labarin faruwar lamarin, sai suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka ɗauki wanda abin ya faru da shi zuwa asibiti, amma da isarsa likita ya tabbatar da ya mutu.

A cewarsa, nan take aka cafke biyu daga cikin wadanda ake zargin, yayin da ƴan sanda suka cigaba da neman sauran.

87 thoughts on “An kashe wani mutumin Bauchi a lokacin da aka zo yi masa gwajin maganin bindiga

  1. Hi, i thin thawt i saw you visited myy site so i came tto “return thhe favor”.I am
    trying tto fnd things tto improvge mmy site!I supppose itts ook to
    use soke oof your ideas!!

Comments are closed.