October 18, 2025

Abba Kabir ya ba wa iyalan ƴansandan da suka rasu tallafi

IMG-20240821-WA0001

Daga Sodiqat A’isha Umar

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa iyalan ’yansandan da suka rasu a hatsarin mota da ya auku a garin Ƙarfi da ke hanyar Zariya zuwa Kano ta’aziya, tare da ba su kyautar naira miliyan 5.2.

Yan sandan sun yi hatsari ne lokacin da suke dawowa daga aikin zaɓen da aka gudanar a Jihar Edo.

Gwamna Abba kabir Yusuf tare da manyan jami’an gwamnatin Kano, ne suka ziyarci ofishin rundunar ‘yan sandan Bichi domin yi musu ta’aziyya kan rasa abokan aikinsu.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu da rahama, ya kuma bai wa waɗanda suka ji rauni sauƙi.

Gwamnan ya kuma bai wa iyalan kowane ɗan sanda da ya rasu kyautar Naira 500,000, sannan ya bai wa waɗanda suka jikkata kyautar Naira 250,000 kowannensu.