Zaki ya hallaka mai kula da shi a Najeriya

Daga Sabiu Abdullahi
A yau ne aka tabbatar da wani Zaki ya kashe ɗaya daga cikin masu kula da shi a cibiyar ajiye namun dawa ta tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da ke birnin Abeokuta a Jihar Ogun.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar, inda Zakin ya yi wasan kura da mutumin, mai suna Babaji Daule mai shekaru 35 wanda a dalilin haka ya ce ga garinku nan.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa babban jami’in tsaro a Gandun Adana Namun Dawar na Obasanjo ne ya sanar da su.
Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ne ya sanya mutumin da lamarin ya rutsa da shi ya yi sakacin barin sakatar da ke killace dq Zakin a cikin keji bayan ya bai wa namun dawar abinci.
Wanda haka ne yasa Zakin damar fitowa kuma ya far wa mai kula da shi, inda ya ji masa rauni a wuya kuma a dalilin haka ya riga mu gidan gaskiya.
Gawar mutumin da zaki ya halaka an ajiye ta a ɗakin killace gawarwaki da ke Babban Asibitin Ijaye.
Takipçi paketi Google SEO, dijital pazarlama stratejimizin temel taşı oldu. https://www.royalelektrik.com/beylikduzu-elektrikci/