A Yi Bincike Mai Zurfi Kan Zargin Da Natasha Ta Yi Kan Akpabio—Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) ta yi na cin zarafi da neman saduwa da ita da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
A yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE a yau Juma’a, Sanata Natasha ta ce tana da shaidu kan zargin da ta ke yi, inda ta bayyana cewa maigidanta ma shaida ne.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu a shafinsa na Facebook a yau, Atiku ya ce dole ne a dauki mataki, domin a binciki lamarin yadda ya dace.
“Kamar miliyoyin ’yan Najeriya, na kalli cikin tsananin damuwa a safiyar yau, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wasu zarge-zargen cin zarafi a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
“Wadannan zarge-zarge suna da girma kuma sun cancanci a yi cikakken bincike na gaskiya da gaskiya.
“Majalisar Dattawan Najeriya ce ke wakiltar muryar jama’a. Wadanda ke aiki a cikinta – musamman shugabanninta – dole ne su kiyaye mafi girman matsayi na mutunci, karamci da mutuntawa, ga ofishinsu da kuma ‘yan Najeriya da su ke wakilta.
“A matsayinsa na mutum na uku mafi girma a kasar nan, ya kamata Shugaban Majalisar Dattawa ya nuna halin da ba za a iya tsige shi ba,” in ji Atiku.
uu7x4f