October 18, 2025

Minista Uche Nnaji Ya Tabbatar Da Cewa Bai Karɓi Takardar Digiri Daga Jami’ar Nsukka Ba

0
images (2) (2)

Ministan Harkokin Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha, Mista Uche Nnaji, ya tabbatar da cewa Jami’ar Najeriya dake Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala digiri ba.

Wannan lamari ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekara biyu da wata jarida ta gudanar, wanda ya gano cewa jami’ar ba ta fitar masa da takardar shaidar kammala karatu ba, duk da cewa ya gabatar da ita ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dattawa lokacin tantance shi a matsayin minista.

Zargin gabatar da takardar bogi ya taso tun cikin watan Yuli 2023, lokacin da Shugaba Tinubu ya sanya sunansa cikin jerin ministoci 28 daga jihohi 25 da aka tura wa Majalisar Dattawa domin tantancewa, bayan kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Wani rahoto ya ruwaito cewa wasu masu suka sun zargi Nnaji da cewa bai kammala karatunsa na jami’a ba, kuma cewa takardun digiri da na bautar ƙasa (NYSC) da ya gabatar wa Shugaba Tinubu, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS), da Majalisar Dattawa, duk na bogi ne.

Sai dai a cewar jaridar, Nnaji a yanzu ya yi magana kai tsaye kan zargin, inda ya amince cewa jami’ar UNN ba ta taɓa ba shi takardar kammala karatu ba.

Amincewar ministan ta fito ne daga wasu takardun kotu da ya gabatar a cikin ƙorafin da ya shigar a gaban babbar kotun tarayya, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Hauwa Yilwa.

A cikin ƙorafin, Nnaji ya nemi kotu ta hana jami’ar UNN yin wani abu da zai bata masa suna ko bayanan karatunsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *