PDP Ta Shirya Tsaf Don Babban Zaben 2027 – In Ji Gwamna Fintiri

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta sake samun ƙarfi kuma ta shirya tsaf don fuskantar babban zaben 2027.
Fintiri ya yi wannan bayani ne a Yola yayin babban taron jam’iyyar na jiha, inda ya ce an gudanar da taron cikin gaskiya da adalci, abin da ya nuna karfin gwiwar jama’a a cikin jam’iyyar.
Ya kara da cewa sabbin shugabannin da aka zaba za su yi jagoranci na tsawon shekaru hudu cikin kwarewa da adalci.
A cewarsa, gwamnati da jam’iyyar na aiki tare domin faranta ran al’umma da kuma tabbatar da shugabanci mai inganci.
Golfa Mallim, wacce ta tsaya takara a kujerar majalisar wakilai ta Guyuk/Shelleng, ta taya sabbin shugabannin murna, inda ta bayyana sabon shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hamza Madagali, a matsayin shugaba mai kishin jama’a da hangen nesa.
Ta ce shugabancinsa zai ƙarfafa jam’iyyar wajen ƙwato kujeru masu yawa a babban zaben 2027.
A taron, PDP ta tabbatar da Alhaji Hamza Madagali a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha, yayin da Saleh Shelleng ya zama sakataren jam’iyyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.