Ƴan Daba Sun Tarwatsa Taron Shawo Kan Matsalar Tsaro A Katsina

Wani taron tsaro da aka gudanar a Katsina ƙarƙashin inuwar Katsina Security Community Initiative ya rikide zuwa tarzoma bayan wasu ƴan daba da ake zargin magoya bayan siyasa ne suka mamaye wurin.
An shirya taron ne domin tattauna hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar, tare da haɗa kwararru daga hukumomin tsaro, tsoffin jami’an soji da ’yan sanda, masana da kuma shugabannin al’umma.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da mai shirya taron, Dr. Bashir Kurfi, yake bayyana matsalolin tsaro a jihar.
Wani daga cikin mahalarta ya katse shi, yana zarginsa da sukar gwamnati.
Daga nan wasu ƴan daba suka tayar da hankula, suka jefa kujeru, suka kai hari ga ’yan jarida, hatta wasu daga cikinsu suna rike da makamai.Bayan da aka tarwatsa taron, masu shiryawa sun yi zargin cewa gwamnati na da hannu a faruwar lamarin.
Sun ce an ga wasu shugabannin ƙananan hukumomi suna tattaunawa da ƴan daban tare da raba musu kuɗi.
Sai dai Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ya bayyana cewa bai da masaniya kan taron, balle abin da ya faru, don haka ba zai yi tsokaci a kai ba.