October 18, 2025

Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta sanar da sabbin alkalai, ta ƙara wa wasu matsayi, ta kuma hukunta wasu

22_49_31_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Bauchi (JSC) ta sanar da nadin sabbin alkalai da karin girman wasu alkalan kotu.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na Hukumar, Dakta Ibrahim Danjuma, Esq., ya fitar a ranar 9 ga Oktoba, 2024.

JSC ta bayyana cewa nadin sabbin alkalai da karin girman wasu suna cikin shirin hukumar na karfafa bangaren shari’a da kuma tabbatar da ingantacciyar hanyar gudanar da adalci a jihar.

Mutanen da aka nada a matsayin alkalai sun hada da: Sadiq Mohammed Abubakar Esq., Aminu Umar Esq., Sani Maigari Isah Esq., Bintu Umar Mustapha, Abdullahi Adarnu Sarki Esq., Ha’inatu Ahmed Esq., da Mohammed Sani Yakubu.

Alkalai masu daraja a Kotunan Shari’a na kasa da aka daga matsayinsu zuwa Alkalai na Kotunan Shari’a na sama sun hada da: Hafizu A. Nuhu, Abdullahi Tijjani, Umar Zakari Yakubu Esq., Dakta Adamu Bello Esq., Nuhu Idris Mohammed, Isa Mohammed Bauchi, da Ibrahim Ibrahim Jibo Esq.

Hukumar ta kuma sanar da ladabtar da wasu jami’an shari’a.

An kori Rabiu Idris Shall, Esq., wanda shi ne babban rajistara, daga aiki saboda yin ba daidai ba da wasu laifuka.

Haka zalika, an tursasawa Saleh Ahmed Fanti Esq., Babban Alkalin Kotun Majistare, yin ritaya saboda aikata laifuka masu tsanani, yayin da aka sauke Hamza Mato Zungur Esq., daga matsayin Alkalin Kotun Shari’a ta Sama, aka mayar da shi ma’aikacin rajista.

Sauran alkalai biyu, wato Mukhtar Muhammad Bello da Mohammed Ismail, sun samu takardun gargadi tare da jinkirta karin girma nasu.

Hukumar ta jaddada kudurinta na tabbatar da cewa bangaren shari’a yana aiki yadda ya kamata tare da tabbatar da adalci da hidimta wa jama’a.