October 18, 2025

Ƴanta’adda sama da 20 sun kashe junansu a wani rikici da ya ɓarke tsakaninsu

FB_IMG_1726246758323

Daga Abdulrazak Namadi Liman

Da sanyin safiyar yau ne wani kazamin rikici ya barke tsakanin ’yan kungiyar ta Mai Nore da kungiyar ta’adda ta Buzaro a yankin Dan-Ali da ke karamar hukumar Dan-Musa a jihar Katsina.

Wasu majiyoyin leken asiri sun shaida muna cewa arangamar ta yi sanadin salwantar rayuka da dama daga bangarorin biyu, inda aka ce sama da gawarwaki 20 aka samu.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana fadan a matsayin mai tsanani, inda aka dauki tsawon lokaci ana ta harbe-harbe a yankin.

2 thoughts on “Ƴanta’adda sama da 20 sun kashe junansu a wani rikici da ya ɓarke tsakaninsu

  1. La vida de Diego Maradona estuvo llena de gloria y controversia | Las frases de Diego Maradona reflejan su amor por el fútbol | El talento de Diego Maradona fue único e irrepetible | Diego Maradona y Lionel Messi siempre han sido comparados Diego Maradona y Messi .

Comments are closed.