Ƴansandan jihar Katsina sun kuɓutar da mutane 30 daga hannun ‘yanbindiga

Daga Abdullahi I. Adam
Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta kuɓutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile hare-haren ‘yan bindiga da dama a wani samame da rundunar ta aiwatar a jihar.
Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a ranar 21 ga watan Agusta lokacin da CSP Bello Abdullahi Gusau, DPO na Dutsinma, ya jagoranci tawagar ‘yansanda da ‘yan banga suka kai farmaki maɓoyar ‘yanbindiga a ƙaramar hukumar Dutsinma.
A yayin wannan samame, an kuɓutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Farar Ƙasa da Shanga da ke ƙaramar hukumar Dutsinma, sannan an kuma samu nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq a ranar Alhamis.
CP Musa ya ci gaba da bayyana cewa, bayan wani ƙazamin faɗa da aka yi a wasu wurare daban-daban a wannan rana, jami’an ‘yansanda sun daƙile harin da ‘yanbindiga suka kai a Malumfashi da ƙaramar hukumar Jibia, inda suka ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su da kuma shanu biyar da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Yaba da ke Malumfashi.
A Jibia kuma, rundunar ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yanbindiga da suka kai hari ƙauyukan Jibian Maje, Nasarawa da kuma Lanƙwasau.
CP Musan ya yabawa bajintar jami’an ‘yansandan da suka yi aikin, sa’annan kuma ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da bayanai kan lokaci don taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka a faɗin jihar.