Ƴansanda sun tura mutumin da ya yi yunkurin kashe kansa wajen gwajin ƙwaƙwalwa a Abuja

Daga Sodiqat Aisha Umar
Rundunar ‘Yansandan ta tura mutumin nan da ya hau kan hasumiyar sabis din gidan rediyo zuwa cibiyar gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa.
A ranar Litinin ne mutumin mai suna Shuaibu Yushau ya hau kan dogon ƙarfen da ke kan dutsen Aso da ke Abuja babban birnin ƙasar, yana mai cewa ba zai sauko ba har sai gwamnati ta sauƙaƙa wa ‘yanƙasa rayuwarsu.
Sai da jami’an tsaro suka shafe lokaci suna lallaɓa shi kafin ya sauko daga kan karfen sabis.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansanda reshen Abuja ta fitar ta ce za su kai shi kotu da zarar an tabbatar lafiyarsa ƙalau.
A Najeriya laifi ne mutum ya yi yunƙurin kashe kan sa.