October 18, 2025

Ƴansanda Sun Kama Ƴansandan Bogi A Kano

images-2025-02-16T132355.305.jpeg

Rundunar ƴansandan Najeriya reshen Kano ta bayyana cewa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da yin damfara ta hanyar sanya kayan ƴansanda na bogi.

Wadanda ake zargin sun damfari wani mutum kudi naira miliyan ɗaya da dubu talatin kafin jami’an tsaro su cafke su.

Rahoton BBC Hausa ya ce an kama mutanen ne a ranar 2 ga Satumba, 2025 a Danagundi Quarters, cikin birnin Kano, kuma dukkaninsu asalinsu daga ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina.Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar da sanarwar da ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sanarwar ta ce, “Kamar yadda bincike ya nuna, an kama su ne bayan wanda suka damfara ya nemi ɗauki, inda ya yi bayanin yadda abin ya faru.

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun yi shigar burtu a matsayin ƴansanda inda suka yi iƙirarin cewa suna da wasu ƙwarewa na musamman da za su taimaka wa wanda aka damfara kuma suka umurce shi ya kai kudin wani wuri.”

Ƴansanda sun ce daukar matakin gaggawa tare da haɗin kan al’umma ya taimaka wajen cafke mutanen da ake zargi.

A halin yanzu bincike yana ci gaba, kuma rundunar ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binciken.