October 18, 2025

Ƴan bindiga sun yi kisar gilla wa masu Maulidi a Katsina

Nigerianbandits-750x375-2.png

Daga Sabiu Abdullahi

Wani gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun afka wa jerin gwanon Mauludi a kauyen Rugar Kusa da ke karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 16 suka samu raunuka a yayin harin.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai da dama, sun isa wurin ne ‘yan mintuna kadan bayan karfe 10 na dare, dauke da muggan makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47.

Sun yi ta harbe-harbe a kan mahalarta taron, inda aka samu asarar rayuka.

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan fashin sun kewaye wurin da ake gudanar da bukukuwan Maulidin inda suka yi ta harbe-harbe ba gaira ba dalili.

Da samun rahoton, jami’an tsaro suka yi gaggawar mayar da martani, inda suka yi nasarar fatattakar maharan.

Nan take aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Musawa don yi musu jinya.

Biyu daga cikin wadanda suka jikkata sun mutu a lokacin da suke karbar magani, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa tara.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa, “har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike, ana ci gaba da kokarin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, za a kuma sanar da su nan gaba kadan.