October 18, 2025

Ƙasar Nikaraguwa ta yanke hulɗar difulomasiyya da Isra’ila saboda abubuwan da ta ƙira “kama-karya” da “kisan kiyashi” a Gaza

15_05_19_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Ƙasar Nikaraguwa ta sanar da shawararta da ta yanke ta katse hulɗar difulomasiyya da Isra’ila tare da yin Allah wadai da gwamnatin Isra’ila da kuma siffanta da aikata “kama-karya” da “kisan kiyashi.”

Wannan matakin ya zo ne bayan da majalisar dokokin Nikaraguwa ta amince da wani ƙuduri da ke neman ɗaukar mataki daidai da lokacin da aka cika shekara guda da yaƙin Gaza.

Gwamnatin Nikaraguwa ta bayyana hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankunan Falasɗinu a matsayin dalilin katse hulɗar.

Yanzu rikicin ya fadada har yana barazanar shafar ƙasashen Labanon, Siriya, Yemen, da Iran, a cewar gwamnatin Nikaraguwa.

Tashin hankalin yankin ya ƙara tsananta bayan harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan Isra’ila a ranar 1 ga Oktoba.

Shugaban Nikaraguwa, Daniel Ortega, yana da alaƙa ta kut da kut da Iran.

Ana kallon wannan mataki a matsayin nuna goyon bayan Nikaraguwa ga sha’anin Falasɗinu da kuma daidaituwar ra’ayi da manufofin ƙasa na Iran.

Har yanzu dai Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare na ta’addanci zuwa ƙasar Lebanon.