October 18, 2025

Yawan Mutanen Da Aka Kashe A Harin Katsina Ya Kai 32

1003352704

Daga TCR HAUSA

Yawan mutanen da aka kashe a harin da ’yan bindiga suka kai yayin sallar asuba a unguwar Mantau, karamar hukumar Malumfashi a Katsina, ya karu zuwa 32.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na safe a ranar Talata, inda ’yan bindigar suka bude wuta a cikin masallaci.

A baya an ce mutane 13 ne suka mutu, amma gwamnatin jihar ta tabbatar cewa 32 aka kashe, wasu kuma aka yi garkuwa da su.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari, wanda ya jagoranci tawagar jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, ya bayyana lamarin a matsayin “mai raɗaɗi da ban tausayi.”

Ya ce gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da kuma hukunta masu laifi.

Kakakin ma’aikatar tsaron cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya ce harin ramuwar gayya ne bayan mutanen Ruwan Sanyi sun kai farmaki kan ’yan bindiga kwanaki kafin haka.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na sojoji da ’yan sanda an tura su tare da fara aikin sama da ƙasa don bin sawun maharan.

Gwamnatin Katsina ta ce tana nan daram kan alkawarin tabbatar da zaman lafiya da kuma tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa.