October 18, 2025

Wata Mai Aikin Shara Da Ta Mayar Da Naira Miliyan 4.8 Da Aka Tura Mata Bisa Kuskure Ta Samu Tallafi Na Naira Miliyan 2.5

1756829809292

Fa’iza Abdulkadir, ma’aikaciyar shara da goge-goge a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, wadda ta mayar da Naira miliyan 4.8 da aka tura mata bisa kuskure, ta sake samun wani tallafi na Naira miliyan 2.5 daga wani mutum da bai bayyana sunansa ba.

An mika mata wannan kyauta ne a ranar Litinin a Maiduguri ta hannun shugabar ƙungiyar Da’awah Wal Irshaad Women Organisation ta jihar Borno, Hajiya Aisha Muhammad Aisami.

Hajiya Aisami ta bayyana cewa mutumin ya karanta labarin Fa’iza a jaridar Daily Trust sannan ya nemi a gano ta domin a karfafa mata gwiwa.

Fa’iza, wadda ke samun albashin Naira 30,000 kacal a wata, na daukar nauyin mahaifiyarta da kuma ‘ya’yanta guda biyar.

A baya matar gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum, ta riga ta yi mata tallafi da Naira miliyan guda, tare da kayan abinci da kuma kayan koyon sana’o’in dogaro da kai.