October 18, 2025

Matashi ya kashe ɗan maƙwabcinsa mai shekara 5

police.jpeg

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Filato sun kama wani dalibi dan shekara 17 mai suna Elijah Anthony bisa zargin kashe yaron makwabcinsa dan shekara biyar bayan ya karbi naira 400,000 a matsayin kudin fansa daga hannun iyayensa.

Anthony, wanda dalibi ne a makarantar Manret High School da ke yankin Angul D a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, yana cikin wasu mutane 39 da ake tuhuma da aikata laifuka daban-daban a hedikwatar ‘yan sanda da ke Jos.

Anthony, wanda ya amsa laifin kashe makwabcin dan shekaru biyar da haihuwa mai suna Dawom Pam, ya ce, “Sun aika da kanensa (wanda aka kashe) ya sayi wani abu, karamin yaron na bayansa. Don haka ni da abokina muka dauke yaron muka boye shi a wani gini da ba a kammala ba

“Daga baya sai iyayen yaron suka zo nemansa, ni ma na yi kamar na haɗu da su wajen neman yaronsu da ya bace amma ban kai su inda aka boye yaron ba.