Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Yunwa A Najeriya

Daga TCR HAUSA
Ofishin hukumar kula da jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana damuwa kan yadda matsalar yunwa, talauci da rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya.
Hukumar ta kiyasta cewa sama da mutane miliyan 31 a ƙasar na fama da ƙarancin abinci.
Haka kuma, hukumar ta ce fiye da yara miliyan 10 ƴan ƙasa da shekara biyar na fama da rashin abinci mai gina jiki.
Wannan bayani ya fito ne a taron da gwamnatin tarayya tare da hukumar suka gudanar a Abuja, yayin bikin ranar Jin-ƙai ta Duniya na 2025 mai taken “Ƙarfafa haɗin gwiwa a duniya da kuma tallafawa al’ummomi”.
Hukumar ta jaddada bukatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage barazanar yunwa da ƙarancin abinci a ƙasar.
Jami’in hukumar a Najeriya, Mohamed Fall, ya ce: “Buƙatar jin-ƙai na ƙaruwa a Najeriya, sakamakon matsalar ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki. Yanzu akwai ƴan Najeriya miliyan 31 da ke fama da matsalar ta ƙarancin abinci.”