October 18, 2025

Kungiyar DWI Ta Soki Atiku Kan Kiran Sakin Nnamdi Kanu Ba Tare Da Sharadi Ba

0
Atiku-Abubakar-900x600-1

Wata ƙungiya mai suna Democracy Watch Initiative (DWI) ta soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa kiran da ya yi na a saki shugaban ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ba tare da wani sharadi ba.

Kungiyar ta bayyana cewa irin wannan kira na iya rage wa jama’a amincewa da bin doka da oda, tare da aikawa da saƙo mara kyau game da gaskiya da adalci.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Dr. Tunji Bamidele, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, DWI ta bayyana cewa kiran Atiku bai dace da matsayinsa na mai fafutukar adalci da haɗin kan ƙasa ba.

Ta kuma shawarce shi da ya sake tunani kan maganganunsa don guje wa abin da zai iya lalata haɗin kan ƙasa.Kungiyar ta ce tana fargabar cewa irin wannan matsayi daga Atiku na iya fassaruwa a matsayin ƙarfafa yin watsi da tsare-tsaren shari’a.

A cewar sanarwar, “Nnamdi Kanu na fuskantar manyan tuhuma, ciki har da ta ta’addanci da cin amanar ƙasa, waɗanda suka haɗa da zarge-zargen tada tarzoma da lalata dukiyar gwamnati da ta jama’a. Waɗannan lamura suna gaban kotu, don haka dole ne a bar tsarin shari’a ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata.”

Kungiyar ta ƙara da cewa, “Kiran sakin Kanu ba tare da sharadi ba na iya haifar da cikas ga tsarin shari’a da kuma ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *