Koriya Ta Arewa Ta Gwada Makaman Kare Sararin Samaniyarta Guda Biyu

Koriya ta Arewa ta bayyana cewa ta yi nasarar gwada makaman kare sararin sama guda biyu a ƙarƙashin kulawar shugaban ƙasar, Kim Jong Un.
A cewar kamfanin dillancin labarai na gwamnati, Korean Central News Agency (KCNA), makaman suna da “nagartar yaƙi” kuma suna aiki da “fasaha ta musamman.”
KCNA ta ruwaito cewa, “gwajin da aka gudanar a ranar Lahadi ya nuna irin ƙwarewar makaman wajen lalata makaman da aka harbo daga sama.”
Wannan lamari ya faru ne ‘yan sa’o’i bayan Koriya ta Kudu ta tabbatar cewa ta yi harbin gargadi ga sojojin Arewa da suka ketare iyaka mai tsananin tsaro na ɗan lokaci.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa kusan sojojin Koriya ta Arewa 30 ne suka tsallaka iyakar ƙasashen biyu kafin daga bisani su janye.