October 18, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

images-2024-12-23T100119.247.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun Laraba, 25 ga Disamba, Alhamis, 26 ga Disamba, 2024, da Laraba, 1 ga Janairu, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bikin Kirsimeti, Boxing Day, da kuma Sabuwar Shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi tunani kan amfanin nuna soyayya, zaman lafiya, da haɗin kai a lokacin bikin.

Dakta Tunji-Ojo ya bayyana muhimmancin wannan lokaci na musamman domin inganta haɗin kai da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin iyalai da al’umma.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban ƙasa don samun cigaba mai ɗorewa.

A wata sanarwa, Ministan ya ce, “Lokacin Kirsimeti dama ce ta tunani na ruhaniya da kuma farfadowar ƙasa. Yayin da muke bikin haifuwar Yesu, Yariman Zaman Lafiya, ya kamata mu nuna alheri tare da ƙara zumunci a tsakaninmu, ba tare da la’akari da banbance-banbancenmu ba.”

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da cigaba a faɗin ƙasa.

Ministan ya bayyana kwarin gwiwarsa kan shirin Gwamnatin Shugaba Tinubu na “Renewed Hope Agenda,” wanda ya ce zai kawo tattalin arziki mai inganci da bunƙasa a sabuwar shekarar 2025.

Daga karshe, ya yi wa ‘yan Najeriya fatan alheri tare da murnar Kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara mai albarka.