Gwamnatin Najeriya Ta Rufe Sama Da Asusu Miliyan 13 A Kafafen Dada Zumunta

Daga TCR HAUSA
Gwamnatin tarayya ta sanar da rufe asusun sada zumunta miliyan 13,597,057 da ake amfani da su wajen yada abubuwan da suka saba doka da kuma cin zarafin jama’a a shafukan TikTok, Facebook, Instagram da X.
Rahoton bin doka na shekarar 2024 da manyan kamfanoni irin su Google, Microsoft da TikTok suka mika wa gwamnati ya nuna cewa an goge abubuwa 58,909,112 da aka dauka a matsayin masu hatsari.
Mai magana da yawun hukumar NITDA, Hadiza Umar, ta ce an samu korafe-korafe 754,629, inda daga ciki aka sake dawo da abubuwa 420,439 bayan masu amfani da shafukan sun daukaka kara.
A cewar sanarwar: “The compliance reports provide valuable insights into the platforms’ efforts to address user safety concerns in line with the Code of Practice and the platforms’ community guidelines.The submission of these reports marks a significant step towards fostering a safer and responsible digital environment for Nigerian users.We remain committed to working with industry players, civil society, and regulatory partners to further strengthen user safety measures, enhance digital literacy, and promote trust and transparency in Nigeria’s digital ecosystem.”Gwamnati ta ce za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin kare tsaron yanar gizo da tabbatar da amincewa da gaskiya a amfani da kafafen sadarwa.