October 18, 2025

Gwamnatin Katsina Za Ta Fara Shirye-Shiryen Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Bindiga

Gunmen-bandit.jpeg

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa za ta kaddamar da wani shiri na musamman domin sauya tunanin tubabbun ƴan bindiga da suka ajiye makamansu, tare da shirya su komawa cikin al’umma cikin zaman lafiya da bin doka.

A cewar gwamnatin, za a bude azuzuwan koyar da ilimi da kuma dabarun sana’o’i ga waɗanda suka miƙa wuya, domin su samu sabuwar rayuwa.

Wannan shiri zai haɗa da koyon karatun zamani da kuma addinin musulunci, don karfafa musu gwiwa su rabu da dabi’un tashin hankali da kuma ɗaukar fansa.

Hukumar ilimin manya ta jihar ce aka dora alhakin tsara wannan tsari, wanda ke da nufin sauya tunanin waɗanda suka taɓa aikata miyagun laifuka, ta yadda za su fahimci muhimmancin zaman lafiya da rayuwa cikin mutunci.

A ƙarƙashin wannan shiri, ana sa ran cewa waɗanda suka miƙa makamansu za su samu horo na musamman da zai basu damar sake rayuwa cikin al’umma tare da dogaro da kai.