Ganduje Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Wata Guda Don Ganin Likita A London

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya daga ƙasar Birtaniya a jiya Laraba bayan ya shafe kusan wata guda yana neman lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa Ganduje ya bar ƙasar nan zuwa London kwana biyar bayan murabus ɗinsa daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulki.
Da yake tabbatar da dawowar tsohon shugaban, tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba, ya bayyana wa manema labarai cewa, “Eh, ya dawo Najeriya yau. Ya dawo cikin koshin lafiya, kuma ya ƙarasa gidansa.”
Garba ya ƙara da cewa tafiyar Ganduje zuwa London ta biyo bayan bukatar samun kulawar lafiya ne bayan saukarsa daga kujerar shugabancin jam’iyyar.