Ficewar Atiku Ba Za Ta Haifar Wa PDP Da Wata Illa Ba – Gwamna Makinde

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam’iyyar PDP ba za ta haifar da wata illa ko tarnaki ga ci gaban jam’iyyar ba.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Ya je birnin ne a matsayin babban bako mai jawabi a wani taron bitar ilimi na musamman da aka shirya domin bikin cika shekaru goma da hawa karagar mulki na Oba Aladetoyinbo Aladelusi, Deji na Akure.
A cewar Gwamna Makinde: “Ina ganin hakan ba zai yi wa PDP wata illa ba. PDP wata cibiya ce, kuma kowa na da ‘yancin shiga da fita.”
A ranar Laraba ne Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a jihar sa ta haihuwa, wato Jihar Adamawa.
Ficewar Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da fargabar rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar, musamman yayin da ƙasar ke shirin fara muhawarar siyasa gabanin babban zaɓen shekara ta 2027.