Fani-Kayode Da Hadimin Tinubu Sun Karyata Zargin Bill Maher Na Kisan Kiristoci a Najeriya

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da mai ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, sun yi watsi da ikirarin da shahararren mai gabatar da shirye-shirye na Amurka, Bill Maher, ya yi cewa ana kisan gilla ga Kiristoci a Najeriya.
A cikin wani bidiyo, Maher ya ce:“Su na kashe Kiristoci a Najeriya ta hanyar da aka tsara. Tun daga 2009 sun kashe fiye da mutane 100,000, sun kuma kona coci 18,000… Wannan ya fi kama da yunƙurin kashe kabilar Kirista gaba ɗaya fiye da abin da ke faruwa a Gaza. A zahiri suna ƙoƙarin share Kiristoci daga duk ƙasar.”
Fani-Kayode ya ce wannan magana “karya ce da aka ƙirƙira” don a bata wa Najeriya suna. A cewarsa:“Ikirarin Bill Maher da American Radio Genoa cewa an kashe Kiristoci 500,000 a Najeriya cikin shekara ɗaya da Musulmi suka yi, ba gaskiya ba ne. Wannan wani shiri ne da kafafen yada labarai na Yahudawa a Amurka suka ƙaraɗe, a matsayin ramuwar gayya saboda matsayinmu kan abin da ake yi a Gaza.”
Ya kuma nuna cewa ta’addanci a Najeriya ba ya tantance addini:“‘Yan ta’addan nan ba sa bambance addini idan suna kashe mutane. Abin da suke so shi ne su kashe mu gaba ɗaya, ko Musulmi ko Kirista, kuma mu ma muna tunkararsu tare da amincewa daya.”
A nasa bangare, Olusegun ya yi suka ga Maher, inda ya ce:“Na yi mamaki ganin yadda ka yi ikirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan ko ana yi musu kisan kare dangi a Najeriya, alhali ba haka ba ne.”
Ya ci gaba da cewa:“Gaskiyar magana, wadda za a iya tabbatarwa, ita ce babu wani shiri na kisan Kiristoci a kowace sassa ta Najeriya, kuma babu wani yunƙuri na kawar da su gaba ɗaya. Wadannan ikirari ƙarya ne masu haɗari, duk da cewa ba sabon abu ba ne, tunda yawan ƙasashen yamma sun saba yada irin wannan labari.”
Olusegun ya kara da cewa tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa ‘yancin addini. Ya ce:“Najeriya ƙasa ce da take koyarwa da yin aiki da juriya tsakanin addinai.”Ya kawo misalin gidan Shugaba Tinubu, inda shi Musulmi ne amma matar tasa fasto ce.
Daga ƙarshe, ya jaddada cewa ba daidai ba ne a fassara matsalar tsaro ta Najeriya a matsayin yaki tsakanin addinai: “Mutanen da ‘yan ta’adda suka kashe a Najeriya sun haɗa Musulmi da Kiristoci. Boko Haram da sauran ƙungiyoyin da suka balle daga gare ta ba su wakiltar Musulunci, kuma shugabannin addinin Musulunci a ƙasar sun dade suna ƙin amincewa da su.”