October 18, 2025

DSS Ta Kama Mutane Biyu Bisa Zargin Damfara Da Sunan Daukar Ma’aikata

images (1) (11)

Daga TCR HAUSA

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta tabbatar da damke wasu mutane biyu a Kaduna da ake zargi da yin damfara ta hanyar bogi wa jama’a da sunan daukar aiki a hukumar.

Wadanda aka kama su ne Aliyu Ibrahim tare da wani abokin harkallarsa. An ce an kama su ne bayan samun bayanan sirri da suka bayyana ayyukansu.

Rahoton farko ya nuna cewa mutane da dama – tsakanin 250 zuwa 350 – na iya kasancewa cikin wadanda aka yaudara da alkawarin samun aikin DSS.

Majiyar tsaro ta ce an riga an tsare mutanen biyu, kuma ana ci gaba da neman sauran wadanda ke da hannu a wannan aiki.

Hukumar ta gargadi jama’a da kada su sake yarda da duk wata sanarwa ta daukar ma’aikata da ba ta fito daga shafukan ta na hukuma ba.

DSS ta kuma roki al’umma da su rika sanar da hukumomi duk wani abu da ya yi kama da dabarar damfara domin kare kansu daga fadawa tarkon ‘yan zamba.