October 18, 2025

An kori jami’in gwamnati saboda ya nemi a tsagaita wuta a Gaza

Sunak.png

Daga Sabiu Abdullahi

An kori wani mai taimaka wa minista a Birtaniya daga mukaminsa na gwamnati bayan ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza.

Gwamnatin Birtaniya ta nuna rashin amincewarta da kalaman da Paul Bristow ya yi, yana mai cewa “ba su yi daidai da ka’idojin gamayyar hadin kai ba”.

A cikin wata wasika da ya aike wa Firai Minista a makon da ya gabata, Bristow ya ce “tsagaita bude wuta na dindindin” za ta ceci rayuka tare da ba da damar taimako ga wadanda suka fi bukata.

Gwamnatin Birtaniya tana goyan bayan “dakatawar al’amurra don kaiwar kayayyakin jin kai” amma ba cikakken tsagaita bude wuta ba.

Duk da haka, Rishi Sunak ya yi watsi da roko na goyon bayan tsagaita bude wuta, yana mai jaddada hakki na Isra’ila na kare kai.