An Tsinci Gawar Kwamandan NDLEA A Otal A Jihar Cross River

Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar Yaki da Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta tabbatar da mutuwar kwamandanta na jihar Cross River, CN Ogbonna Maurice Uzoma, wanda aka samu gawarsa a wani otal da yake Calabar.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an samu rahoton lamarin ne daga shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), a yayin da yake halartar taron shugabannin hukumomi da ma’aikatar shari’a ta tarayya ta shirya a Maiduguri, jihar Borno.
A cewar Babafemi, an nada marigayin a matsayin kwamandan Cross River a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, kuma tun daga lokacin ya soma gudanar da aiki da jajircewa.
Ya zauna a wani otal a Calabar kafin ya sami masauki na dindindin.
Rahoton ya ce an shirya Ogbonna zai jagoranci wasu ayyuka da safiyar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025, amma daga karfe 9 na safe ba a sake jin duriyarsa ba.
Wannan ya sa jami’ansa tare da ma’aikatan otal suka nufi dakinsa, sai dai duk bugun kofa da kiran wayarsa bai amsa ba.
Daga baya wani ma’aikacin otal ya shiga ta saman rufin dakin ya bude daga ciki, inda aka tarar da shi ya riga mu gidan gaskiya.
Nan da nan aka sanar da rundunar ‘yansanda, inda kwamishinan ‘yansanda na jihar ya kai ziyara da kansa.
Shugaban NDLEA ya umarci kwamandan yankin, ACGN Mathew Ewah, da ya koma Calabar domin kula da bincike kan lamarin.
Yayin jajantawa ga iyalan marigayin, Janar Marwa, ya bayyana cewa hukumar na tare da su a wannan mawuyacin lokaci, tare da yi musu addu’ar Allah Ya jikan mamacin.