Ƴan Fashi Sun Yi Ajalin Ɗalibin Makarantar ATAP Da Ke Bauchi

An sake samun mummunan al’amari a garin Bauchi, inda ƴan fashi suka kai wa ɗaliban Abubakar Tatari Ali Polytechnic (ATAP) farmaki, makonni biyu kacal bayan makamancin irin wannan ya faru a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Jihar Bauchi.
Rahotanni sun ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe uku na tsakar dare a ranar Juma’a, lokacin da wasu ƴan fashi uku suka kutsa ɗakin kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar, inda suka tarar da ɗalibai biyu a ciki.
A yayin arangama, ɗaya daga cikin ɗaliban, Samuel Mbami, ɗalibin ND2 a sashen Koyar da Harkokin Yaɗa Labarai (Mass Communication), ya samu mummunan rauni sakamakon caka masa wuka a ciki.
Ya rasu daga baya saboda yawan zubar jini.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Dalibai na makarantar (SUG), Usman Aliyu, ya fitar, ƙungiyar ta yi Alla-wadai da wannan harin, tana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da rashin imani.
Ƙungiyar ta kuma bukaci hukumomi da su gudanar da cikakken bincike tare da ƙara tsaurara matakan tsaro a cikin makaranta da kewaye, domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
Haka zalika, Ƙungiyar Ɗaliban ta yi kira ga sauran ɗalibai da su kwantar da hankalinsu tare da kula da tsaron rayukansu.